fidelitybank

NDLEA ta lalata ganyen Wiwi kilo 7,286 a Edo

Date:

Gabanin babban zaɓen 2023 da ke tafe a ranar Asabar, jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA, ta bayyana lalata ganye mai sa maye mai nauyin kilogiram 7,286 bayan yin dirar miƙiya a wani gandun dajin Ujiogba da ke jihar Edo.

A wata sanarwa da darektan yaɗa labaru na hukumar ya fitar a shafinta na twita, ya ce ta gudanar da samamen ne a ranar Laraba bayan samun bayanan sirri da ke cewa masu tu’ammali da kwayoyi sun shiga dajin rike da ɗaruruwan jakukkunan ganyen domin rarrabawa zuwa wasu jihohi gabanin gudanar da zaɓen.

Karanta Wannan: NDLEA ta kama hodar ibilis da za a mika kasashen waje

NDLEA ta ce sai da jami’anta suka shafe tsawon lokaci suna artabu da ‘yan bindiga da kuma manya masu safarar ƙwayoyi kafin ta samu nasara a kansu, inda bayan nan ta cinna wuta kan wasu jakukkunan tabar wiwi da dama, tare kuma da tafiya da wasu guda bakwai domin gudanar da bincike da hukunta waɗanda ake zargi.

Ta kuma ce ta ƙwato bindiga ƙirar AK47 da wasu ƙananan bindigogi da kuma harsasai, inda suka kama wani ɗan shekara 24 mai suna Calvary Essien da ake zargi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyin.

Da yake mayar da martani, shugaban hukumar, Birgediya-Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen da kuma wasu kusan 10,000 da aka tura zuwa faɗin jihohi domin sa ido gabanin zaɓe wajen ganin ‘yan bangar siyasa basu yi amfani da ƙwayoyi ba kafin da lokaci da kuma bayan zaɓe.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp