Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA reshen Apapa Legas, ta ce, ta ƙwace miyagun ƙwayoyi na kimanin Naira biliyan shida tsakanin watan Janairu zuwa Yunin bana.
Kwamandan hukumar reshen Apapa, Ameh Inalegwu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa nauyin ƙwayoyin da suka ƙwace ya kai kilo 19,703.25.
Ya kuma bayyana cewa rundunarsa a shirye take domin ta shawo kan matsalar miyagun ƙwayoyi da ake shiga da su ƙasar ta teku.
Ya ce, cikin miyagun ƙwayoyin da aka kama har da tramadol da hodar ibilis da codeine.