Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta NDLEA, ta kai samame tare da ƙona wuraren ajiyar tabar wiwi a wasu dazukan jihar Edo da ke kudu maso kudancin ƙasar.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta ƙona tabar wiwi da nauyinta ya kai tan 317 a gidajen ajiye kayyaki tare da kama mutum huɗu da take zargi da hannu.
Haka kuma ta ce a wani samame na haɗin gwiwwa da hukumar EFCC sun samu nasarar kama kuɗaɗen ƙasar Amurka na jabu da suka kai dala 269,000.