Jamiāan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, sun kama wani Dattijo mai suna Aliyu Adebiyi dan shekara 67, wanda a gidansa suka gano tabar wiwi kilogiram 234 a kauyen Sokoto, Owena Ijesa, a karamar hukumar Atakumosa ta Gabas ta jihar Osun. Kakakin hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.
A cewarsa, wanda ake zargin, a cikin bayaninsa, ya ce, wani dillalin miyagun kwayoyi ya ajiye kayan a wurinsa akan kudi naira 6,000 duk wata kuma ya biya na tsawon watanni uku a gaba.
Hakazalika, an kama wani kuturu da ya yi kaurin suna wajen safarar miyagun kwayoyi, Haruna Abdullahi, mai shekaru 45 a garin Garko, jihar Kano a ranar Alhamis 19 ga watan Janairu, yayin da aka kwato kilogiram 2.2 na tabar wiwi da Diazepam da Exol daban-daban daga gare shi.
Moreso, Babafemi ya kuma bayyana cewa, an sake samun ci gaba a kokarin da ake yi na shigo da hodar iblis da skunk 126.95kgs cikin Najeriya da aka boye a cikin buhunan shayi na ganye da kuma motocin da ke shigowa da su daga Brazil da Canada a filin jirgin saman Akanu Ibiam International Airport (AIIA), Enugu da kuma Jami’an NDLEA na tashar jirgin ruwan Tincan dake Legas.
āA filin jirgin saman Enugu, an kama wani fasinja mai suna Eze Christian Ikenna, dan shekara 42, wanda ya shiga wani jirgin saman Ethiopian Airline da ya taho daga Brazil ta hanyar Addis Ababa, Habasha, lokacin da ya isa filin jirgin da karfe 12:30 na ranar Jumaāa, 20 ga watan Janairu. A binciken da aka yi wa buhunan sa guda biyu, an gano manyan buhuna guda 19 da ya yi ikirarin cewa suna dauke da shayin ganye amma daga baya aka gano cewa hodar iblis ce mai nauyin kilogiram 16.20,ā inji shi.