fidelitybank

NDLEA ta kama tarin kwayoyi da za a yi safarar su zuwa Australia, China, Qatar

Date:

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wasu adadi mai yawa na Methamphetamine, Cocaine, da Cannabis sativa da aka shirya don fitarwa zuwa kasashen Australia, China, Qatar, Ireland da Thailand ta wasu kamfanonin jigilar kayayyaki a Legas.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, jami’an na hukumar ta DOGI ne suka samu nasarar hakan.

Ya ce, yayin da aka kama kilo 2.9 na Methamphetamine a cikin fakitin baƙar miya da injin toner da ke kan hanyar zuwa Australia da Qatar; Giram 600 na Cocaine wato hodar Iblisi da aka boye a cikin takardun makaranta da ke zuwa Australia da Thailand an kama su daidai.

Babafemi ya kara da cewa, an kuma kama tabar wiwi kasa da ta kai kilogiram 25.5 da aka boye a cikin fakitin sabulun Dudu Osun da dalolin dabino (banga) da ke kan hanyar zuwa kasashen China da Ireland a wani kamfanin jigilar kayayyaki da ke Legas.

A halin da ake ciki, an kwato kilogiram 2,293.324 na haramtattun kwayoyi da kuma Naira 791, 100 a wasu manyan samame da jami’an tsaro suka kai a jihohin Ogun, Ribas da Enugu a cikin makon da ya gabata.

A cewar Babafemi, a Ribas, a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, jami’an tsaro sun kai samame a sannnaniyar ruwa ta Abuja da ke birnin Fatakwal, bayan bayanan da aka kama suka bayar, kan hanyoyin samar da kayayyaki.

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp