fidelitybank

NDLEA ta kama mutanen da take nema ruwa a jallo

Date:

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wasu mutane da ta shafe wata biyu tana farautarsu bayan da ta zarge su da ƙwarewa wajen safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu da Mozambique da ƙasashen Turai da Amurka.

Cikin wata sanarwa da hukumar ke fitarwa mako-mako, da mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya aike wa da BBC ya ce hukumar ta kama mutanen ne bayan kama wata hodar ibilis mai yawa a filin jirgin sama na Legas.

Sanarwar ta ce hukumar samu nasarar kama biyu daga cikin mutanen da ta jima tana nema ruwa-a-jallo, watao Onyinyechi Irene Igbokwuputa da kuma Frankline Uzochukwu ranar Juma’a 19 ga watan Afrilu a filayen jirgin saman Legas da na Awka.

Sai kuma Osita Emmanuel Obinna wanda ta kama shi a birnin Legas.

Hukumar ta NDLEA ta kuma ce takama wani mutum da ya yi yunƙurin fita da tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 9.80, daga Najeriya zuwa ƙasar Oman.

”Bayan hukumar ta kama shi ya bayyana cewa an ƙulla yarjejeniyar cewa za a biya shi naira miliyan 1,200,000 idan har ya fitar da tabar zuwa Oman”, in ji sanarwar.

Babafemin ya kuma ce a ranar 20 ga watan Afrilu hukumarsa ta kama wani direban mota a Girei kan hanyarsa ta zuwa Mubi, inda jami’an hukumar suka kama ƙwayar ‘opioids’ da ke sa maye da yawanta ya kai miliyan 1,250,000 mai nuyin kilogiram 450.

daily post nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp