Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kaduna, ta ce jamiāanta sun kama mutane 90 da ake zargi tare da tarwatsa gidajen miyagun kwayoyi guda 13 a Kaduna.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Mista Samaila Danmallam, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a ranar Lahadi, cewa an kama tare da tarwatsa gidajen haramtattun kwayoyi a cikin watan Nuwamba.
Danmallam ya kuma bayyana cewa a cikin wannan wata an kama wasu haramtattun abubuwa masu nauyin kilogiram 478.038.
A cewarsa, daga cikin mutane 90 da aka kama, 85 maza ne yayin da biyar kuma mata ne.
Ya ce an ci gaba da kokarin rage bukatun muggan kwayoyi na rundunar tare da bayar da shawarwari da shirye-shirye daban-daban a fadin jihar.
Danmallam ya ce an yi hakan ne domin fadakar da āyan kasar kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi.
Kwamandan ya bukaci iyaye da su kasance masu lura da unguwanninsu a koda yaushe.
Danmallam ya kuma yi kira da a samar da bayanai masu amfani kuma a kan lokaci domin daukar matakan da suka dace, inda ya bukaci yaki da fataucin miyagun kwayoyi da shan miyagun kwayoyi ya zama wani nauyi na hadin gwiwa.


