Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta kama ƙunshin hodar ibilis ko kuma koken a filin jirgin sama na Fatakwal da ke Jihar Rivers a kudancin Najeriya.
NDLEA ta wallafa wani bidiyo da ta ce yana nuna yadda masu safara suka ɓoye ƙunshi 73 na koken ɗin a cikin zanin gado.
Kazalika, hukumar ta ce ta ƙwace ƙwayar tramadol miliyan tara da rabi a Legas da ta kai darajar naira biyan biyar.
Hakan nan, hukumar ta ce, ta kama mutum bakwai a Kano, saboda zargin su da mu’amala da miyagun ƙwayoyin.