Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Kano ta kama mutane akalla 319 da ake zargi a fadin jihar tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2024.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Mista Abubakar Idris-Ahmad, wanda ya bayyana haka a wata hira da NAN a ranar Litinin, ya ce hukumar ta kuma kama tan 4.7 na haramtattun kwayoyi.
A cewarsa, wadanda ake zargin sun kasance maza 305 da mata 14.
Ya ce an kama kimanin kilogiram 2.3 na tabar wiwi da kuma kilogiram 2.4 na abubuwan da suka shafi kwakwalwa daga hannun wadanda ake zargin a cikin lokacin da aka kama su.
Idris-Ahmad ya ce jami’ansu sun kuma kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan biyar da kuma 1.9kg na wasu abubuwa masu hadari.
A cewarsa, a cikin watanni ukun, rundunar ta kama wasu mutane 33 da ake zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi da sauran laifukan da suka shafi muggan kwayoyi.
“Mun gyara masu shaye-shayen miyagun kwayoyi guda 26, mun aiwatar da takardar izinin shiga 38, mun kuma gudanar da gwajin ingancin kwaya guda 30 ga daidaikun mutane da mambobin majalisar masarautun jihar.”
Kwamandan ya kara da cewa, a tsawon lokacin da rundunar ta yi nazari a kai, ta kori gidajen haramtattun kwayoyi guda 39 da ke zama cibiyar ayyukan ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.
Idris-Ahmad ya baiwa mazauna Kano tabbacin daukar kwararan matakai na tabbatar da an gudanar da bukukuwan lafiya ba tare da shan miyagun kwayoyi ba a yayin bukukuwan Sallah-El-Fitr da ke tafe.
“Hukumar ta himmatu wajen tabbatar da doka da oda a wannan lokaci na bukukuwa da kuma hana yaduwar miyagun kwayoyi a cikin al’umma,” inji Idris-Ahmad.K