fidelitybank

NDLEA ta kama mawakan gambara da tabar Wiwi a Legas

Date:

Hukumar da ke yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa, ta kama wasu fitattun mawaka biyu na Gambara da wasu mutane hudu dauke da muggan kwayoyi a wani samame da suka kai musu a wani gida da ke cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Legas a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Femi Babafemi ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an samu wasu nau’ukan tabar wiwi tare da mawakin Gambara na rap wato Zinoleesky da Mohbad da wasu mutane hudu da ake zargi a gidansu da motarsu.

“Jami’an mu sun kai farmaki gidan da ke cikin Estate Idado da sanyin safiyar yau,” in ji shi.

“An kama mutane shida, maza hudu mata biyu. An kwato wasu adadin tabar Wiwi daga gidansu da motarsu. “

Babafemi ya ce, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike.

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp