Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wani matashi mai suna Nabala Mustapha, dan shekara 25, da busasshiyar tabar wiwi sativa 1kg.
Kamen wanda Eden Shem Lama ya jagoranta ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a unguwar Mararaba da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.
David Yamsak Milaham, babban jami’in hukumar ta NDLEA ne ya bayyana yadda aikin ya gudana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Wanda ake zargin dan asalin karamar hukumar Igabi ne a jihar Kaduna, an tsare shi ne a yayin wani hadin gwiwa da jami’an NDLEA suka yi.