fidelitybank

NDLEA ta kama matasa 111 da safarar mugan kwayoyi a Kaduna

Date:

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta jihar Kaduna ta bayyana cewa, ta kama mutane 111 masu safarar miyagun kwayoyi, tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairun 2022 a jihar.

Kwamandan rundunar, Umar Adoro, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ranar Alhamis, a Kaduna.

Ya ce, yawancin wadanda ake zargin sun kai shekaru 16 zuwa 30.

Ya bayyana cewa an kama mutane 34 a watan Janairu daga cikinsu 31 maza ne, yayin da uku kuma mata ne, ya kara da cewa an kuma kama kwayoyi masu nauyin kilogiram 295.680.

“Mun kama 292.125kg na Cannabis Sativa, 0.001kg na Heroin da 3.554kg na abubuwan da ke damun kwakwalwa kamar Benalin, tramadol da sauransu.

“A watan Fabrairu, mun kama mutane 77 da ake zargi daga cikinsu 74 maza ne yayin da uku kuma mata; kuma an kama jimillar kwayoyi 320.508,” inji shi.

Adoro ya bayyana cewa daga cikin adadin magungunan da aka kama 294.101kg sun hada da Cannabis Sativa, 0.034kg Cocaine, 0.005kg Heroin yayin da 26.358kg na psychotropics da 0.010kg Methamphetamine.

Ya kara da cewa, hukumar ta kuma gano wani sabon alkalami mai dandanon Shisha, wanda dandanonsa na dauke da man wiwi, wanda matasa ke amfani da shi.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp