Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA za ta kona hodar iblis da sauran miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai naira biliyan 193 a Lagos.
Hodar iblis din na cikin wawan kamen miyagun kwayoyin da hukumar ta yi a makon jiya.
Hukumar NDLEA ta ce ta kama hodar iblis mai yawan kilogiram 1,855 tare da cafke wasu masu safarar kwaya lokacin da ta kai samame wani gidan ajiyar kaya a yankin Ikorodu na jihar Lagos.
Ga kamen da hukumar ta ce shi ne guda daya mafi girma a tarihin yaki da miyagun kwayoyi na Najeriya, ta wargaza shirin safarar kwayoyin da suka kai kimanin naira biliyan 194.
Hukumar ta kuma ce ta kama dillalan kwaya hudu ciki har da wani dan kasar Jamaika da manajan gidan ajiyar kayan.