Jami’an Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, sun kama hodar ibilis da wasu muggan ƙwayoyi masu yawa da aka yi niyya shigar da su Turai a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke birnin Legas.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta ce ta ƙwace kilogiram 75.75kgs na tabar wiwi da aka shigar da ita ƙasar a ɓoye cikin kwantaina daga Canada.
Karanta Wannan: Ba a kama dan Najeriya da kwaya ba a aikin Hajjin bara – NDLEA
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an hukumar sun kama wata mace mai ciki, da wani malamin makaranta, tare da ƙwace tan biyu na muggan ƙwayoyin a jihohin takwas da ke ƙasar.