Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kama wani mutum da ake zargin yana daga cikin fursunonin da suka tsare a lokacin da aka kai hari gidan yarin Kuje.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumakar Femi Babafemi ya fitar ya ce sun kama mutumin da safiyar ranar Litinin a lokacin da yake kokarin hawa motar Maiduguri a tashar mota ta Area 1 da ke Abuja babban birnin kasar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne hukumomin gidan yarin na Kuje suka wallafa sunaye da hotunan fursunoni 68 wadanda ta ce mayakan Boko-Haram ne, suke zargi sun tsere a lokacin da aka kai wa gidan yarin hari a makon da ya gabata.
Hukumar NDLEA ta ce ta samu mutumin da raf uku na tabar wiwi a lokacin da suke bincikensa.