Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta kama wani babban faston majami’ar The Turn of Mercy Church, Adefolusho Olasele, kan zarginsa da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi daga Ghana zuwa Najeriya.
An kama Olasele ne wanda ya shafe tsawon watanni yana tserewa hukumomi a ranar Lahadi, 3 ga Agustan 2025 – a cocinsa da ke Okun Ajah, a jihar Legas.
Wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, ya ce jami’an hukumar sun jira sai da faston ya gama wa’azinsa kafin daga bisani suka cafke shi lokacin da yake barin harabar cocin.
A cewar Babafemi, faston ya tsere zuwa Ghana a watan Yuni, bayan da jami’ai suka alaƙanta shi da wasu ganyen wiwi da aka kama mai nauyin kilogiram 200 a bakin ruwa na Okun Ajah ranar 4 ga watan Yuni da kuma wanda aka samu a cikin motarsa.
Babfemi ya ce malamin majami’ar ya amsa cewa yana safarar ƙwayoyi ta ruwa daga Ghana zuwa cikin Najeriya.