fidelitybank

NDLEA ta kama fasfo din kasashen waje a cikin buhun Gari

Date:

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama fasfo din kasa da kasa guda 22 na kasashe shida daban-daban da aka boye a cikin buhun Gari da dai sauran kayayyakin abinci.

Jami’an tsaro sun kama su ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International na Ikeja dake jihar Legas, a harabar tashar SAHCO da ke filin jirgin a lokacin da suke aikin binciken kayan da suka saba yi.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin, ya ce tara daga cikin fasfo din uku ne kowannen su na Birtaniya da Faransa da Portugal da na Najeriya 8 da Ghana 4 da kuma na Kamaru 1.

Ya kuma ce a filin jirgin, jami’an sun kwato fakiti 12 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 4.95 da aka boye a cikin kwalin Golden Morn da aka shirya domin fitar da su ta cikin rumbun ajiyar kayayyaki na SAHCO.

A halin da ake ciki, Babafemi ya bayyana cewa, a jihar Filato, tawagar jami’an NDLEA a ranar Juma’a 28 ga watan Janairu, sun kama wasu mutane biyu da ake zargi ciki akwai Emeka Ezenwa mai shekaru 37 da Julius Akingbe mai shekaru 45 da haihuwa, bisa laifin mallakar gram 126.5 na sinadarin methamphetamine da aka boye a cikin na’urar DVD da ta taho daga Legas.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp