Kimanin mutane 164 da ake zargin dillalan miyagun kwayoyi ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama a jihar Filato.
Muhammad Abba, mataimakin kwamandan, a ranar Alhamis, ya bayyana hakan a Jos yayin da yake zantawa da manema labarai.
Ya yi bayanin cewa, “Hukumar NDLEA ta kuma kama haramtattun kwayoyi 417.136 daga hannun masu safarar miyagun kwayoyi a jihar.”
Ya ce an kama 414kg na hemp na Indiya, 1.061kg na tramadol, 2.625kg na diazepam, 32.5g na flunitrazepam, 6.6g na rohypnol da 4.6g na codeine daga hannun dillalan jami’an NDLEA.
Ya kuma bayyana cewa tuni hukumar ta fara gudanar da bincike kan wadanda ake zargin, inda ya bada tabbacin za a gurfanar da su a gaban kotu.