Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ta ce, ta cafke wasu kayayyaki da aka shiga da su Najeriya daga waje a filin jirgin sama na Legas.
Cikin kayayyakin da hukumar ta ce ta kama, akwai kwalaben maganin kodin (codeine) guda 1,730.
Haka kuma, NDLEA ta ce, ta kama wani mutum mai suna Muhammad Yusuf da ƙwayar tramadol 8,000 a cikin wata motar fasinja a kan hanyar Kano – Katsina.
NDLEA ta kuma ce a ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu, jami’anta a Kaduna sun kai samame wani ɗakin gwaje-gwaje na ɓoye inda suka kama muggan ƙwayoyi a Sabon Garin Zariya, tare da kama mai ɗakin gwaje-gwajen, mai suna Christopher Agodi.
Haka kuma, a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, jami’an tsaro sun kama wani mai suna Atiku Abubakar, mai shekaru 22 da jakunkunan tabar-wiwi guda 50 mai nauyin kilogiram 28, yayin da yake tafiya daga Legas zuwa Shinkafi na jihar Zamfara a cikin wata motar bas.


