fidelitybank

NDLEA ta cafke kwayoyin da aka shigo da su daga Brazil da Canada

Date:

Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta ce ta samu nasarar kama hodar ibilis da tabar wiwi da aka shiga ƙasar da ita daga ƙasashen Brazil da Canada a a biranen Enugu da Legas.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya sanya wa hannu, ta ce hukumar ta kama ƙwayoyin tramadol miliyan 1.7 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar, tare da kama mutanen da ta daɗe tana nema a jihohin Osun da Kano da Ondo da Edo da Abuja babban birnin ƙasar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”Jami’an hukumar NDLEA da ke aiki a filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu da masu aiki a tashar jirgin ruwa na Tican da ke Legas sun samu nasarar daƙile yunƙurin shigo da kilogiram 126.95 na hodar ibilis da tabar wiwi ƙunshe cikin ƙwalayen ganyen shayi da ababen hawa daga Brazil da Canada”.

Sanarwar ta ƙara da cewa a filin jirgin saman Enugu an kama wani fasinja mai suna Eze Christian Ikenna mai shekara 42, da ya shiga ƙasar daga Brazil ranar 20 ga watan Janairun, bayan da aka binciki jakar da ya zo da ita inda ka samu hodar ibilis da ta kai nauyin kiligiram 16.2.

nnn-news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp