Mahukunta a Najeriya sun bankado kunshin kwayar crystal methamphetamine da aka boye a kan wani kifi da aka sanya a cikin kwalin da za a kai shi Hadaddiyar Daular Larabawa.
A ranar Juma’a ne aka gano kunshin wanda nauyinsa ya kai kusan kilogram 12 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Hukumar hana sha da fataucin miyagin kwayoyi ta kasarce ta sanar kama kwayar a ranar Lahadi.
Hukumar ta ce, an samu kunshi-kunshin kwayar 442 kowannesu an nade shi da leda a kan bushasshen kifin da aka zuba su a kwalaye za a fita da su.
Tuni aka kama mutumin da ke da kwalayen kifin.


