fidelitybank

NDLEA ne suka yi min gadar zare bayan na ƙi bayar da ladan gabe – Abba Kyari

Date:

Babban jami’in ‘yan sandan Najeriya da aka dakatar ya musanta zargin alakanta shi da kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa.

An kama Abba Kyari ne a makon da ya gabata bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar NDLEA ta zarge shi da alaƙa da wata kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke aiki tsakanin Najeriya da Habasha da kuma Brazil.

Sai dai a ranar Litinin ya shaidawa wata kotu a Abuja babban birnin kasar ta hannun lauyoyinsa cewa ƙirƙirar zargin aka yi.

Hukumar NDLEA ta yi zargin cewa Mista Kyari ya yi yunkurin bai wa jami’anta cin hanci don kilo 25 na hodar ibilis da jami’ansa suka kama sannan suka raba.

Sai dai Abba Kyari ya musanta zargin cewa, jami’an hukumar NDLEA ne suka masa gadar zare bayan ya nace sai an bayar da lada ga wanda ya bayar da labarin da ya kai ga kama waɗanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi kamar yadda suka amince da farko.

Ɗaya daga cikin lauyoyinsa, Hamza Nuhu Dantani, ya shaida wa BBC cewa, sun kuma gabatar da bukatar neman belinsa.

daily post newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp