Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta ayyana neman fitaccen mamallakin Otal din Adekaz, Ademola Kazeem, ruwa a jallo bisa zargin safarar miyagun kwayoyi da halasta kudin haram.
Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi, ya ce matakin bayyana nemansa ruwa a jallon ya biyo bayan rashin amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.
Mista Femi ya ce hukumar na zargin mista Ademola da daukar nauyin wasu masu safarar kwayoyin da hukumar ta kama suna yunkurin fitar da kwayoyin zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen duniya.
Ya kara da cewa “Bayan da muka kama wani direba wanda yaronsa ne mai suna Bolujoko Muyiwa Babalola, a watan Yuni ranar 27 ga watan Yuni a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da Legas, sai Alhaji Ademola Kazeem wanda shi ne shugaban kamfanin Adekaz Global Integrated Services ya yi batan dabo”.