Sifeto Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Baba Alkali, ya yi kira ga Shugaban hukumar hana fasa kwabrin muggan kwayoyi, Janar Buba Marwa ya damke jami’ansa dake taimakawa masu safarar kwaya tare da Abba Kyari.
Shugaban ‘yan sandan ya bayyana hakan ne a jawabin da kakakin hukumar ya saki ranar Litinin yayinda ya ke sanar da damke Abba Kyari.
A cewar Legit, IGP Alkali ya ce, hasali ma jami’an hukumar NDLEA sun karbi cin hanci hannun masu kwayan kuma sun barsu sun wuce.
Ya yi kira ga Janar Buba Marwa ya gudanar da binciken kansa kuma ya damke na hukumarsa, inda gaskiya za’a yi.
Yace: “Binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa, masu safarar kwayoyin na da alaka mai karfi da jam’an NDLEA a tashar jirgin saman Akamu Ibiam dake Enugu, saboda suna biyansu kudade. Masu safarar kwayoyi biyun da aka kama sun tabbatar da cewa sun dade suna harka tare da jami’an NDLEA tun 2021, kuma a kan lamarin 19 ga Janairu, 2021, an barsu sun wuce da kwayoyin.”