Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta cafke wanda ya taso daga kasar Brazil da ya dawo gida, Igwedum Uche Benson, a dakin taro na filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA), Ikeja, Legas, dauke da kwalayen hodar iblis da aka boye a al’aurarsa.
An kama Benson ne a ranar Litinin 20 ga Yuni, 2022 lokacin da ya iso kan jirgin Habasha daga Sao Paulo, Brazil, ta Addis Ababa.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya hadiye kwalaye 50 na hodar iblis kafin ya tashi daga kasar Brazil, sannan ya fitar da pellet 48 a Addis Ababa, inda ya mika su ga wani mutum.