Kocin Leicester City, Brendan Rodgers yana da kwarin gwiwar cewa Wilfred Ndidi zai samu damar buga wasan Premier da Nottingham Forest a daren Litinin.
Dan wasan ya samu karamin rauni a wasan da Leicester City ta doke Nottingham Forest da ci 6-2 makonni biyu da suka gabata.
Ndidi ya dawo da wuri daga buga wasan kasa da kasa a makon jiya sakamakon koma bayan da ya samu.
Rodgers dai yana fatan dan wasan na Najeriya zai samu damar buga wasan da za su kara da Steve Cooper.
“Mun sa Wilfred Ndidi ya dawo da wuri,” Rodgers ya fada wa wani taron manema labarai ranar Juma’a.
“Yana da kyau sosai kuma ya sami horo a safiyar yau da fatan zai yi kyau.”
Har yanzu Leicester City tana neman nasarar farko a kakar wasa ta bana.
Foxes sune kasan log É—in tare da maki É—aya daga wasanni bakwai.