Hukumar Sadarwa ta kasa NCC, ta shirya bai wa kamfanonin sadarwa a kasar wa’adin kwanaki 30, domin shawo kan duk wasu matsaloli da masu amfani da layuka da sauran hanyoyin sadarwa ke fama da su.
A cewar hukumar, idan mai amfani da layi ya mika ƙorafinsa amma aka ƙi a saurare shi, zai iya sanar da ita bayan kwanaki 30, inda ita kuma za ta dauki matakin da ya dace.
An dai bayyana hakan ne cikin wani sabon daftarin dokokin ayyuka na hukumar da aka ɗora a shafinta na Internet.
Masu amfani da wayoyin hannu a Najeriya dai sun jima suna ƙorafi kan yadda kamfanonin layuka a ƙasar ke nuna halin ko in kula da ƙorafe-ƙorafensu.