Hukumar da ke sa ido kan harkar sadarwa ta kasa NCC, ta tabbatar da rufe layukan masu wayoyin salular da basu haɗa da lambar shaidar zama ɗanƙasa ba.
A makon da ya wuce ne hukumar ta bai wa kamfanonin wayoyin salula umarnin rufe layin duk wani wanda bai haɗa layin wayarsa da NIN ba ya zuwa ranar 28 ga watan Fabairun, 2024.
Wasu kafofin watsa labarai na ƙasar sun ce waɗanda lamarin ya shafa sun kai miliyan 11 da dubu 200.
Sai dai wata hira da wani gidan talabijin na cikin ƙasar, kakakin hukumar , Reuben Muoka ya ce zai yi wuya a ce ga yawan layukan da aka rufe, amma NCC za ta yi kididdiga kafin ƙarshen wannan makon, bayan sun samu alƙaluma daga kamfanonin sadarwar.
“A ɗauka cewa duk wani wanda bai bayar da NIN ɗinsa ba an rufe layinsa. A haƙiƙanin gaskiya ma tun kafin cikar wa’adin wasu kamfanonin sadarwan suka fara rufe layukan mutane. Ya shaida wa Channels TV.
Haka kuma ya yi tsokaci kan wasu masu wayoyin da suka ce sun riga sun haɗa NIN ɗinsu da lauyukansu amma duk da hakan an rufe layukansu, inda ya ce an rufe wasu layukan ne saboda ta yiwu NIN ɗin da suka bayar bai zo daidai da wanda suka yi rajista ba.
Masu irin waɗan nan matsaloli a cewarsa, dole su je kamfanonin sadarwar da kansu domin a gyara matsalolin.
A baya dai hukumar ta sha sanya ranar rufe layukan mutanen da basu haɗa da lambar shaidar zama ɗanƙasar ba, sai dai a wannan karon ta ce babu batun ɗagewa.