Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta (NBC), ta tsawaita wa’adin biyan bashin da ta saka wa kafofin labaran da ta ƙwace wa lasisi.
A ranar Juma’a ne NBC ta ƙwace lasisin aiki na kafofin yaɗa labaran fiye da 50 saboda abin da ta ce sun kasa biyan bashin da take bin su kuma ta ba su awa 24 su yi hakan.
Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, hukumar ta ce ta ƙara wa’adin zuwa ranar Laraba, 23 ga watan Agustan 2022 maimakon kwana ɗaya, inda ta umarce su da su biya kuɗin.
“Dukkan kafofin labaran da suka gaza biyan bashinsu, an umarce su da su kulle daga ranar 24 ga Agusta, 2022,” a cewar sanarwar da shugaban hukumar Balarabe Shehu Ilelah ya sanya wa hannu.
Daga cikin kafofin da NBC ta ƙwace musu lasisi akwai: gidan talabijin na AIT, Silverbird TV, Raypower FM, Rhythm FM.
Hukumar ta ce, tana bin gidajen labaran kudin da suka kai naira biliyan 2.66 don sabunta lasisin nasu.


