Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa (NBC), ta dakatar da rufe gidajen yada labarai da ake bi bashi a fadin kasar nan.
A ranar 19 ga watan Agusta ne hukumar NBC ta sanar da soke lasisin gidajen Talabijin mai zaman kanta na Afrika (AIT), da gidan talabijin na Silverbird da kuma wasu gidajen watsa labarai 50 saboda rashin biyansu kudaden sabunta lasisi.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Darakta Janar na NBC Balarabe Shehu ya ce Hukumar ta yanke shawarar dakatar da rufe gidajen rediyon.
Shehu ya bayyana cewa dakatarwar ta wucin gadi ce.
Ya kuma danganta dakatarwar da taron da NBC ta gudanar da shuwagabannin kungiyar yada labarai ta Najeriya (BON) da sauran masu ruwa da tsaki a harkar.
NBC DG ya nuna godiya ga BON, masu lasisin da abin ya shafa da masu ruwa da tsaki na masana’antar watsa shirye-shirye don amsawa da shiga tsakani.
Wasu sassan sanarwar sun ce, “Hukumar yada labarai ta kasa, a ranar Juma’a, 19 ga watan Agusta, 2022, ta bayar da sanarwar rufe lasisin da ke bin hukumar bashi.


