fidelitybank

NBC ta ci tarar Talabinjin din Arise a kan kalaman tunziri

Date:

Hukumar da ke kula da kafofin yada labarai ta NBC, ta ci tarar gidan talabijin na Arise naira miliyan biyu bayan samunta da laifin yaɗa kalaman da za su tunzura ‘yan ƙasa.

A cikin wata sanarwa da NBC ta fitar wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar Balarabe Shehu Ilelah, ta ce an kama gidan talabijin ɗin da laifi ne bayan da ya watsa wata magana da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi a ranar 24 a watan Febrairu, inda yake suka ga magoya bayan jam’iyyar APC.

NBC ta ce a cikin maganganu da Wike ya yi ya ce “Ni ba ɗan APC bane kuma ba zan shiga jam’iyyar ba, amma sun sanya na amince da su a matsayin jajirtattu, don haka mulki ya koma kudu”.

Sanarwar ta NBC ta ƙara da cewa Arise ya kuma saka wata tattaunawa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a daidai lokacin da ake kaɗa kuri’a a ranar zaɓe wanda abu ne da ya saɓawa dokokin hukumar.

Har ila yau, ta ce gidan talabijin ɗin ya gayyato baki da dama waɗanda suka yi kalamai na tunzura ‘yan ƙasa zuwa cikin rikici.

NBC ta kuma ce cikin laifukan da Arise ya yi, akwai saka wakar wani ɗan Najeriya mai suna Fela Kuti da ke magana kan batun maguɗin zaɓe da kuma cin hanci, inda ta ce bai kamata gidan talabijin ɗin ya saka wakar a lokacin ba saboda ana cikin zaɓe.

A don haka, NBC ta ce ta ci tarar gidan talabijin naira miliyan biyu saboda aikata waɗannan laifuka da suka saɓawa dokokin kafafen yaɗa labaru a ƙasar.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp