Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta Nato, Jens Stoltenberg, ya ce, kungiyar na duba yiwuwar sake aika Karin makamai domin taimakawa Ukraine a yakin da take da mamayar Rasha a kasarta.
Ya ce, aikin Nato ne ta taimakawa Ukraine kuma suna yin haka da taimakon makamai na zamani, da kudade da taimakon soji da kuma agaji.
Jens Stoltenberg ya yi gargadin cewa, Rasha ba ta da niyyar tsagaitawa, sannan babban burinta a yanzu shi ne ta karbe ikon ilahirin yakin Donbass da ke gabashi nan da makonni masu zuwa.
Rundunar sojin Ukraine ta ce dakarun Rasha na sake gina kansu a kokarin kai sabbin farmaki, sannan rahotanni da ake samu na baya-bayanan na cewa suna ta ruwan wuta a birane irinsu Kharkiv da Luhansk da Donetsk.
Kokarin kwashe fararan hula daga yankunan da ake yaki na fuskantar cikas.