fidelitybank

NATO ta yi tsit da kiran Ukraine

Date:

Kungiyar tsaro ta NATO ta ki amincewa da rokon da Ukraine ta gabatar mata na sanya dokar hana shawagin jiragen sama a wasu sassan kasar domin kare jama’a daga hare-haren sama na Rasha.

BBC ta rawaito cewa, kungiyar na cewa hakan ka iya sa yakin ya fantsama a Turai.

Bayan ganawa da ministocin harkokin waje na kasashen Turai, babban Sakataren kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce an cimma matsaya cewa jiragen saman yaki na kungiyar da dakarunta ba za su yi aiki a yanki ko sararin samaniyar Ukraine ba.

Mista Stoltenberg ya yi kira ga Rasha da ta dakatar da hare-haren da take kaiwa

Ya ce ”tun watanni da dama, muka yi gargadi cewa Shugaba Putin na da niyyar mamaye Ukraine. Abin da ya sa kenan kawayen NATO suka yi ta kai gauro suna kai mari domin samar da maslahar diflomsasiyya”.

A hakan kuma muka yi gargadin cewa Rasha za ta dandana kudarta a kan sabbin hare-haren da take kai wa Ukraine.

Kasashen NATO da dama na ta aika wa Ukraine makamai, sannan kuma kungiyar na karfafa tsaronta a baryar gabas.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp