Sakatare-janar na kungiyar tsaro ta NATO, Mark Rutte, ya taya Donald Trump murnar lashe zaben shugaban kasar Amurka.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Rutte, a cikin sakon taya murna, ya ce komawar Trump kan karagar mulki zai taimaka wajen ci gaba da karfafa kawancen.
“Jagorancinsa zai sake zama mabuɗin don ƙarfafa ƙawancen dangantakarmu.
“Ina fatan sake yin aiki tare da shi don ciyar da zaman lafiya ta hanyar karfi ta hanyar NATO,” in ji shi.