fidelitybank

Natasha ta halarci zaman kotu tsakanin ta da Akpabio

Date:

Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattijai, Natasha Akpoti-Uduaghan ta halarci zaman kotu a shari’ar da take ƙalubalantar dakatarwar da aka yi mata daga majalisar.

A watan Maris ne majalisar dattijan ta dakatar da Natasha bisa zargin rashin ɗa’a bayan taƙaddamar da ta kaure tsakaninta da shugaban majalisar Godswill Akpabio.

A cikin ƙorafinta, Natasha ta haɗa majalisar tarayya da majalisar dattawa da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da kuma Sanata Neda Imasuen, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ladabi da haƙƙoƙi da ɗabi’a a matsayin waɗanda ake ƙara.

Lokacin da aka kira shari’ar, wadda aka mayar a hannun Justice Binta Nyako bayan Justice Obiora Egwuatu ya janye daga sauraron ta, lauyan Sanata Natasha, Jibrin Okutekpa, ya shaida wa kotu cewa sun gabatar da dukkan takardun da za su dogara da su a shari’ar, kamar yadda kotu ta umarta a zaman da ya gabata.

Lauyoyin da ke wakiltar majalisar dattawa, Paul Daudu, da na shugaban majalisar, Ekwo Ejembi, su ma sun shaida wa kotu cewa sun gabatar da takardun da za su dogara da su. Amma sun jawo hankalin kotun kan wani buƙata da suka shigar dangane da rashin bin umarnin kotu da suke zargin wanda ke karar da aikatawa.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, a cikin wa’adin martaninta na ƙari, ta zargi shugaban majalisar dattawa da ƙoƙarin tauye mata haƙƙinta na faɗin albarkacin baki

Ta ce wasikar da ta rubuta kwanan nan zuwa ga shugaban majalisar dattawa ba ta karya umarnin kotu ba, wanda ya haramta wa ɓangarorin da ke cikin shari’ar yin magana da kafafen yaɗa labarai.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...

Tarayyar Turai tamince da ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da ƙaƙaba wa Rasha...

Gwamnan Filato ya zargi Jami’ai da kin kama ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Filato ta zargi jami'an sojojin ƙasar da...

Za a yi wa Buhari addu’a a Abuja

Gwamnatin Tarayya za ta jagoranci gudanar da taron addu'o'i...

Buhari ya ban umarni na kula da Talakawan Najeriya – Peter Obi

Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce,...

Sojojin hadin gwiwa sun hallaka ‘yan Boko Haram a tafkin Chadi

Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a...

Na yi rashin aboki na gari kuma Najeriya ta rasa mutumin kirki – Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na ci gaba da alhinin...
X whatsapp