Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar da komawa bakin aiki, inda ta bayyana cewa ba ta da hurumin komawa har sai an kawo ƙarshen dakatarwar da aka yi mata.
A wata sanarwa da kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ya fitar ranar Lahadi, ya jaddada cewa babu wani umarnin kotu da ya ce majalisar ta karɓi Sanata Natasha kafin ƙarewar lokacin da aka dakatar da ita.
An dakatar da sanata Natasha ne tun watan Maris ɗin 2025 sakamakon karya dokokin majalisar bayan ta yi gardama da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio – inda ta zarge shi da cin zarafi ta hanyar lalata, abin da Akpabio ya musanta.
A kwanakin baya, Natasha, wadda ta dogara da hukuncin da mai shari’a Binta Nyako na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke, ta bayyana niyyarta ta komawa zauren majalisa ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025.
Sai dai, kakakin majalisar dattawa ya ce hukuncin ba ya ɗauke da wani umarni na doka da ya ce majalisar ta karɓi dawowar sanatar kafin karewar wa’adin dakatarwa da aka yi mata.