Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce jihar Nasarawa ta jam’iyya ce mai mulki.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga mabiya jam’iyyar a liyafar da aka shirya don karrama shugaban jam’iyyar APC na Nasarawa, Hon. Aliyu Bello, a Lafia, babban birnin jihar.
Ganduje ya kuma sha alwashin kare zaben Abdullahi Sule.
“Mun ci zabe, kuma za mu kare hakkinmu. Babu shakka game da shi.
“Jihar Nasarawa ta APC ce, kuma APC ta jihar Nasarawa ce. Mu ne a kan mulki, kuma za mu ci gaba da kasancewa da ikon Allah,” inji shi.
Ku tuna cewa a kwanakin baya ne kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta bayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben.


