Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya taya gwamna Hope Uzodinma da Usman Ododo murnar nasarar da suka samu a zaben da aka kammala a jihohin Imo da Kogi, bi da bi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Uzodinma da Ododo ‘yan takarar jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka lashe zaben gwamna da aka gudanar a jihohin Imo da Kogi ranar Asabar.
Sanata Barau, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya bayyana nasarorin Uzodinma da Ododo a matsayin nuna kwarin guiwar al’ummar jihohin biyu kan shirye-shirye da manufofin jam’iyyar APC.
Nasarorin da ya samu, ya ce za su baiwa Gwamna Uzodinma damar hada ayyukan raya kasa a jihar Imo da kuma Ododo domin ci gaba da shirye-shiryen tallafawa jama’a na Gwamna Yahaya Bello a jihar Kogi.
“Nasarar kuma ta samo asali ne daga jagororin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban babbar jam’iyyarmu ta kasa, Dakta Addullahi Umar Ganduje, wanda ya kara hada kan jam’iyyarmu,” inji shi.