Kwamitin zaman lafiya mai kula da kyautar Nobel ya ba da shelar cewa wata ƴar kasar Iran, mai fafutukar kare haƙƙin mata, Narges Mohammadi ce ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a bana.
Kwamitin ya ce ta samu kyautar ne saboda fafutukar da take yi a kan cin zarafin mata a Iran da kuma kokarinta na inganta ‘yancin ɗan’adam da ‘yancin kowa da kowa.
Narges Mohammadi ƴar kasar Iran ce mai fafutuka kuma mataimakiyar shugaban cibiyar kare hakkin bil adama, wadda wani da ya taɓa lashe kyautar Nobel a kan zaman lafiya, Shirin Ebadi ya kafa.
Narges Mohammadi ta fuskanci hukuncin dauri da dama tun daga shekara ta 2011 kuma a halin yanzu tana tsare a gidan yarin Evin da ya yi kaurin suna a Tehran a kan tuhumar “yaɗa farfaganda”.
A bana kuma, an saka ta a cikin shirin mata 100 na BBC- shirin da ya kunshi jerin manyan mata 100 masu kokarin zaburar da mutane da kuma karfin faɗa-a-ji daga ko’ina a fadin duniya.
A yayin da ake sanar da lashe kyautar, kwamitin Nobel ya ce “jajircewarta da gwagwarmayarta ne suka sanya ta cancancin lashe kyautar”.