fidelitybank

NAPTIP ta kuɓutar da ƴan Najeriya tara da aka yi niyyar safarar su zuwa Libya

Date:

Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya, NAPTIP ta ce ta kuɓutar da wasu ƴan Najeriya da aka yi niyyar safararsu zuwa Libya.

Kwamandan hukumar a jihar Zamfara, Aliyu Abubakar ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen tara ne a iyakar Babura da ke jihar Jigawa, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

Aliyu ya ce akwai mata guda uku cikin mutanen tara – waɗanda ƴan asalin jihar Zamfara ne.

Sun tserewa gidajensu ne sakamakon hare-haren ƴanbindiga, inda suka koma zama a Kaduna.

NAPTIP ta ja hankalin mutane kan faɗawa makomar masu safarar mutane – inda ta ce kowa ya yi taka tsantsan.

Safarar mutane dai ba sabon abu bane a kan iyakokin Najeriya, inda a watan Fabrairu, gwamnatin jihar Neja ta karɓi yara 21 da hukumar shige da fice ta kuɓutar da su – waɗanda ba su haura shekara tara ba lokacin da ake tafiya da su Nijar.

nigeria news today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp