Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP), ta kama wani matashi dan shekara 26, bisa laifin safarar mutane a Awka, babban birnin jihar Anambra.
Kwamandan hukumar ta NAPTIP a jihar, Misis Judith-Chukwu Ibadin, wacce ta bayyana hakan ga manema labarai a jiya, ta ce, an kama wanda ake zargin, Franklin Onyebuchi tare da hadin gwiwar hukumar shige da fice ta ƙasa.
A cewarta, Onyebuchi dan asalin jihar Imo ne, amma yana zaune a Onitsha, inda ta kara da cewa an kama shi ne da laifin daukar wata mata ‘yar shekara 20 (an boye sunanta) ga wani daya da ake zargi da safarar mutane a Dubai.
Wanda ake zargin yana aiki ne tare da hadin gwiwar kungiyoyin sa da ke jihar Edo da kuma birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
“Wanda ake zargin ya yaudari wanda aka kashe daga jihar Edo zuwa Anambra, kuma an kama shi a ofishin Immigration da ke Awka, a lokacin da yake sarrafa fasfo na kasa da kasa na Najeriya, domin a kai shi Dubai.