Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) reshen jihar Kano, ta ceto mutane goma da aka yi safarar mutane a hanyarsu ta zuwa jamhuriyar Nijar, domin yin aikin kwadago.
Ko’odinetan Hukumar NAPTIP shiyyar Arewa maso Yamma, Abdullahi Babale ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Babale ya ce, an dauki mutanen ne daga jihohin Kogi, Delta, Kwara, Oyo, Ondo, Legas, Ogun da kuma Osun.
Ya ce wadanda abin ya shafa na tsakanin shekaru 9 zuwa 28 ne yayin da biyu daga cikinsu maza ne takwas kuma mata ne.