Victor Osimhen ya yi la’akari da cewa Napoli na gab da lashe Scudetto gasar Serie A, bayan lallasa Torino da ci 4-0 a ranar Lahadi.
Yanzu dai kungiyar Luciano Spalletti ta samu tazarar maki 21 akan Lazio mai matsayi na biyu bayan nasarar da suka yi a filin wasa na Olimpico Grande.
Partenopei na karshe ya lashe kambun shekaru 30 da suka gabata tare da marigayi Diego Armando Maradona ya taka muhimmiyar rawa.
Karanta Wannan:Â Arsenal ta shiga zawarcin Osimhen
“Muna kusa da Scudetto kuma muna so mu ci nasara ga magoya bayanmu,” Osimhen ya shaida wa shafin yanar gizon kulob din.
Dan wasan mai shekaru 24 ya zura kwallaye biyu a ragar Torino inda ya sake jaddada mahimmancinsa ga nasarar kungiyar a kakar wasa ta bana.
Ya zuwa yanzu dan wasan ya ci kwallaye 21 a wasanni 23 da ya buga wa Napoli a wannan kakar.