Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana kwarin gwiwar cewa, nan ba da dadewa ba za ta karbe iko da jihar Ribas.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka a wani taron da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Ganduje ya jaddada cewa za a sake gina reshen jam’iyyar a jihar Ribas tare da mayar da hankali wajen kafa sansani a jihar.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da dan takarar gwamna na jam’iyyar Action Alliance (AA) a 2023, Dawari Ibietela George, ya koma APC a hukumance.
A yayin tattaunawar tasu, shugabannin sun mayar da hankali ne wajen sake gina jam’iyyar reshen Jihar Ribas tare da mayar da ita wani dandali na yi wa al’ummar jihar da kasa hidima yadda ya kamata.
Ganduje ya bayyana kudirin jam’iyyar na rungumar bukatu daban-daban tare da tabbatar da adalci.
Ya bayyana George a matsayin babban kifi, ya kuma yaba wa hazakarsa ta siyasa, inda ya nuna kwarin gwiwa kan yadda zai kara karfin jam’iyyar.
Ganduje ya yi maraba da George, inda ya tabbatar masa da cewa za a kafa wani tsari mai inganci da zai dauki nauyinsa da sauran mambobin da suka dawo.
“Jihar Rivers za ta zama jam’iyyar APC gaba daya. Yanzu kun kasance daidai da kowane dan jam’iyya. Mun himmatu wajen fadada dimokuradiyya a kasar nan,” Ganduje ya kara da cewa.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin gwamnan jihar, Sim Fubara da kuma magabacinsa, Nyesom Wike, wanda a yanzu yake rike da mukamin ministan babban birnin tarayya karkashin gwamnatin APC, dangane da wanene ke rike da tsarin jam’iyyar a jihar.