Bayan yanke hukuncin ƙarshe da Kotun ƙolin Najeriya ta yi, wanda ya tabbatar da kujerun gwamnonin jahohin adawa na Kano da Zamfara da Filato da Bauchi, jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar ta ce hakan bai razana ta ba.
Jami’yyar ta ce akwai rata mai nisa tsakaninta da sauran jam’iyyun adawa kasancewar yawan jihohin da take da su, duk da ana ganin nasarorin da jam’yyun adawar suka samu a kotun koli ta kara masu karfi.
A wata hirar da ya yi da BBC wani jigon jam’iyyar ta APC kuma , karamin ministan gidaje da raya birane Injiniya Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce duk wani gunagunin da ake yi lokaci ne zai tabbatar da asalin yadda lamura suke da kuma irin ƙarfin da jam’iyyar take da shi a siyasance.
Ministan ya ce duk maganganun da ake ta yaɗawa game da jam’iyyar gabannin yanke hukuncin kotun duk labarai ne na ƙanzon-kurege, kuma asalin bayanai za su bayyana nan gaba.
‘Ana cewa mun rasa Jihohi, ai ba rasa su muka yi ba, harka ce ta kotu, abin da kotu ta zo da shi, mu ma mun shiga kuma an shigar da mu, saboda haka mun yi nasara a wasu kuma a wasu mun yi rashin nasara. Yanzu APC muna da jiha 20 mai bi mana PDP tana da 13, APGA na da ɗaya Labour na da ɗaya, NNPP na da ɗaya, to me za mu ƙyasa a ciki? Jn ji shi.