Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa, za a samar da Man Fetur (Premium Motor Spirit) a kasuwannin Najeriya nan da sa’o’i 48, ya danganta da Kamfanin Man Fetur na Najeriya.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wata hira da gidan talabijin na Channels, yayin da a hukumance ya sanar da fara fara fitar da man fetur daga matatar mai da ke Legas 650,000 a kowace rana ranar Talata a Legas.
Ya jaddada cewa nan ba da jimawa ba matatar mai na dala biliyan 20 za ta kammala tattaunawa da kamfanin na NNPC domin isar da kayan ga ‘yan Najeriya.
Da yake magana kan farashin man fetur din Dangote ya bayyana cewa shi ne tsarin majalisar zartarwa ta tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ne za ta yanke hukunci.
“PMS na iya kasancewa a gidajen mai a cikin sa’o’i 48 masu zuwa, ya danganta da NNPCPL.
“A kan farashin PMS, tsari ne wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya karkashin jagorancin Mai Girma, Bola Ahmed Tinubu ta tsara kuma ta amince da shi. Da zaran an kammala, wanda shi ne abin da yake turawa da zarar ya kammala taron FEC, zai iya zama yau ko gobe a shirye mu ke mu fito kasuwa.” Inji shi.
Tun da farko dai Dangote a hukumance ya sanar da fara fitar da mai a ranar Talata.