fidelitybank

Nan ba da daɗe wa ba wa’adin NNPP zai ƙare – Ganduje

Date:

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ba ta aiki kuma nan ba da dadewa ba za wa’adin ta zai kare.

A cewar Ganduje, NNPP ta mutu kuma Rabiu Kwankwaso dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023 yana son dawowa APC.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi magana a ranar Talata a Abuja, lokacin da ya karbi tawagar Tinubu Support Group, TSG, a sakatariyar jam’iyyar.

Ya ce jam’iyya mai mulki za ta shirya tsaf domin tarbar Kwankwaso da hannu biyu-biyu.

Ya ce, “Jam’iyyar NNPP ta mutu, kuma nan ba da jimawa ba za a yi jana’izar ta, ina duba inda za mu binne gawar, an riga an gina akwatin gawar.

“Abin da ya rage a yanzu shi ne tono kabari, kuma tuni sun fara tono kabarin nan ba da dadewa ba.

“Ko da haka, wanda ake kira shugaban NNPP na kasa, shi ma ya ce bayan ya rasa kowa, yana so ya dawo wurinmu, za mu yi masa maraba, domin yana dawowa gida,” in ji shi.

A halin da ake ciki, Kwankwaso da NNPP sun sha musanta ikirarin sauya sheka da APC ke yi.

Da yake jawabi yayin taron majalisar zartarwa ta kasa NNPP a Abuja kwanan baya, Kwankwaso ya ce Ganduje ne zai hada shi a NNPP ba wai akasin haka ba.

 

taraba state today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp