Gwamnatin Brazil ta sanar da cewa Najeriya ta amince ta shiga cikin ƙungiyar ƙasashen duniya da ake yi wa laƙabi da BRICS.
Brazil, wadda ita ce ke shugabantar ƙungiyar a 2025, a cikin wata sanarwa, ta bayyana cewa Najeriya “ta ƙasance ƙasa da ke ƙara ƙarfafa hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen ɓarin kudancin duniya da kuma sauya salon shugabanci”, wanda abu ne da Brazil ke bai wa muhimmanci.
“A matsayinta ta ƙasa ta shida mafi yawan al’umma a duniya, kuma mafi yawan al’umma a Afirka, kuma ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka, Najeriya na da kamanceceniyar manufofi da ƙasashen ƙungiyar,” kamar yadda sanarwar ta ma’aikatar harkokin waje ta Brazil ta sanar.
BRICS, ƙungiya ce ta ƙasashen da suka haɗa ba Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta kudu, Masar, Habasha, Indonesia, Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Ana wa ƙungiyar kallon kishiya ta ƙungiyar ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi ta duniya, wato G7.