Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta na shirin kwashe wasu ma’aikata ƴan Najeriya da suka makale a yankin Bambari da ke Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya bayan da aka bar su ba tare da kulawa ba.
Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta fitar a ranar Juma’a ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Bangui sun tuntubi mutanen da abin ya shafa kuma suna aiki tare da hukumomin cikin gida don tabbatar da lafiyarsu da kuma dawowarsu gida cikin gaggawa.
Ma’aikatar ta kuma shawarci ’yan Najeriya da ke neman aiki a ƙasashen waje su duba sahihancin masu ɗaukar aiki da kuma tabbatar da cewa dukkan takardunsu sun cika kafin tafiya.