Kungiyar Falconets ta Najeriya za ta kara da Burundi a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya na mata na ‘yan kasa da shekaru 20 na shekarar 2024.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF ce ta gudanar da jadawalin a hukumance a birnin Alkahira na kasar Masar.
Za a buga wasannin farko da na biyu tsakanin 6 ga Oktoba zuwa 15 ga Oktoba.
Wadanda suka yi nasara a karawar za su wuce zagaye na uku na wasannin share fage da aka shirya yi tsakanin 12 ga watan Nuwamba zuwa 19 ga Nuwamba.
Kasashe biyu ne za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya.
Falconets sun kasance a matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta karshe.